Yadda aka kama malamin jami’a akan gado tare da ɗalibarsa

An gabatar da malamin jami’ar ‘Kwara University’ mai suna Pelumi Adewole a gaban kotu inda ake zarginsa da neman lalata da ɗaliba.

Malamin ya shiryawa ɗalibar sake rubuta jarabawarta ne a ɗakinsa.

Sai dai tuni ta kaiwa hukuma ƙaransa inda tace ya mata barazanar kayar da ita jarabawa idan bata biya masa buƙatarsa ba.

Malamin dai bai daɗe da yin aure ba, inda a watan Yuni da ya gabata ne ya zama ango.

Jami’an tsaro sun gayawa ɗalibar ta bi malamin har inda ya nemeta dan a samu shaida a kansa, inda aka kamashi yana ƙoƙarin lalata da ɗalibar.

Kotu dai ta bayar da belinsa akan naira 200,000 da kuma wani da zai tsaya masa. An ɗaga ƙarar zuwa 8 ga watan Satumba.

Views: 20

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *