
Rahotanni daga jihar Gombe sun bayyana cewa, wani bawan Allah ya bude ma’adanar hatsin sa inda yake siyar da shi a kan farashi mai sauki fiye da na kasuwa.
Rahotannin sun ce, Wani Bawan Allah Mai Suna Alh. Sagiru Muhammad Ya Fito Da Masara Yake Sayarwa Da Talakawa Akan Farashin Kwano Ɗaya ₦200 A Garin Gombe.
Najeriya dai na fama da tsadar farashin kayayyakin masarufi dana bukatun yau da kullum, duk kuwa da cewa wannan ba sabon al’amari bane amma mafi yawanci masu hali suna sassauto da farashin kayan masarufi amma yawanci anfi ganin hakan a lokacin watan Ramadana.
Wanne Fata Kuke Dashi Ga Wannan Bawan Allahn?
Views: 16
