Daga shafin Rariya, Wallahi Ba Da Sanin Mijinta, Hafsat Ismail Tuge Ta Shiga Harkar Fim Ba
Daga Ismail Sumaila
Masu cewa shi mijin yana ina? Ya kamata komai mu rika yin bincike idan ba mu san me ya faru ba.
Wallahi mijinta bai sani ba, saboda dan kasuwa ne, kuma ba ya ma kallon fim kwata-kwata, kullum yana wurin harkokin kasuwancinsa.
A makon da ya gabata ne wata ‘yar uwarsa ta kira shi take gaya masa, a lokacin ma ya san me yake faruwa, saboda a yankin Gwarzo take aure sai ta ce masa za ta je cikin garin Kano ziyarar kanwar mahaifiyar ta, kuma ka ga ba zai hana ta zumunci ba, idan ta zo sai ta je ta ci gaba da fim din ta.
Tuni ma ya sa Daraktan fim din a kotu, inda a yau Talata za a fara sauraren shari’ar a nan Kano.
Views: 26
