An turo labarin ne a wani dandalin sada zumunta na facebook mai suna SIRRIN ƴa macce inda mai labarin ta nemi da a sakaya sunanta ga dai goton abinda take cewa nan daga ƙasa.

A wani labarin kuma
BADAƘALA: An Sauke Ali Baba Fagge Daga Shugaban Dattawan APC
Kwamitin Dattawan jam’iyyar APC a reshen ƙaramar hukumar Fagge a jihar Kano, (Caucus) sun dakatar da shugabansu, SA Ali Baba Agama Lafiya Fagge bisa zarginsa da danne musu haƙƙoƙinsu da yayi har karo biyu.
A cikin wata takarda mai ɗauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a na kwamitin da mataimakinsa, Salisu Shitu da Shehu Sani Chidozie, da aka aikewa shugaban ƙaramar hukumar Fagge, Ibrahim Muhammad Shehi, sun bayyana cewa Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya basu Naira Miliyan daya (N1,000,000) da Sallar da ta gabata ta hannun dakataccen shugaban nasu, amma shiru bai basu ba.
Sanarwar da aka fitar ta ƙara da cewa, kwanan nan ma jam’iyya ta basu Motoci guda Ashirin domin halartar taron zuwan ɗan takarar shugabancin Nijeriya na Jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, na ziyarar kwanaki biyu da yayi a Kano, shima dai shiru bai basu haƙƙin su ba.
A baya dai cikin shekarar 2020 (Ranar Arfa) aka zargi mai baiwa gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje shawara akan harkokin addinai, Ali Baba Agama Lafiya Fagge, da saka ɗansa Huzaifa Ali Baba, ya karbe kuɗi N50,000 da gwamna ya bawa malamai na addu’ar Allah ya kawar da Korona da kuma nemawa Kano zaman lafiya, ya basu N5,000 kowannensu, duk da kashedin da gwamna yayi akan kada wanda ya karɓi wani kaso cikin malaman, amma Ali Baba yayi burus sai da ya karba.
Malam Ali Baba ya amsa wannan zargi tun a wancan lokaci, amma yace anyi hakan ne don a faɗaɗa abin, kasancewar akwai wasu malaman da sukayi addua a gida, kuma dama a haka aka tsara za’a basu cikin kuɗin da aka bawa wadanda suka je gidan gwamnati, abinda yasa shugaban hukumar karɓar ƙorafe-ƙorafe da yaƙi da cin hanci da rashawa ta jihar Kano na wancan lokacin, Barista Muhuyi Magaji Rimin Gado, yayi sammacin Ali Baba da ɗansa Huzaifa, kuma aka dawowa da malaman kuɗinsu, duk da dai babu wani matakin doka da aka ɗauka a kansu.
DAGA Abubakar Lecturer
Views: 33
