Shahararren ɗan daudunnan na Duniya wanda ya sauya fasalin halittar sa daga Namiji zuwa macce wato Bobrishki ya bayyana cewa yana da juna biyu.
Dama a watan disambar daya gabata ne aka ambato shi yana cewa ya fara jinin al’ada kamar yadda mata ke yi sai gashi a halin yanzu yace yana da ciki.
A wani labarin kuma.
Gwamnatin tarayya ta tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa za a gudanar da babban zaɓen ƙasar da ke tafe kamar yadda aka tsara.
Ministan yaɗa labarai Lai Mohammed na ya bayyana haka a Abuja, a lokacin gabatar da ci-gaban da ma’aikatarsa ta samu ƙarƙashin gwamnati mai ci.
A lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai game da kalaman da wani babban jami’i a hukumar zaɓen ƙasar ya yi na cewa zaɓen ƙasar na fuskantar barazanar sokewa saboda matsalar tsaro.
Ministan ya ce matsayar gwamnati ita ce zaɓen 2023 zai gudana kamar yadda aka tsara.
Ya ƙara da cewa ”babu abin da ya faru da ya sauya wannan matsayi.
Mun sani cewa INEC na aiki da jami’an tsaro domin tabbatar da samun nasarar gudanar da zaɓen a faɗin ƙasar”.
“Hukumomin tsaro na ci gaba da aiki ba dare ba rana domin tabbatar da cewa an gudanar da zaɓukan cikin kwanciyar hankali. Dan haka babu wata fargaba”, in ji ministan
Hukumar Zaɓe dai ta saka ranar 25 ga watan Fabrairu a matsayin ranar da za a gudanar da zaɓen shugaban ƙasa a Najeriya.
jabiralidanabba
NasaraRadio
AmanarTalaka
Views: 25
