Wani matashi ya bayya cewar ya sayi jirgi da kuɗin Pi-Network.
A wani labarin kuma
Gwamnatin Kano ta tabbatar da bullar cutar diphtheria a kananan hukumomi 13.
Gwamnatin jihar Kano ta tabbatar da bullar cutar diphtheria a kananan hukumomi 13 na jihar.
Kwamishinan lafiya na jihar, Dr Aminu Tsanyawa ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai kan ɓullar cutar zazzaɓin Diphtheria da Lassa a jihar a jiya Asabar.
Ya ce an samu mutane 100 da a ke zargin sun kamu da cutar, inda uku su ka mutu.
“Ya zuwa ranar 20 ga watan Janairun 2023, mun samu rahoton bullar cutar guda 100 da ake zargi daga kananan hukumomi 13.
”Ungogo, Nassarawa, Bichi, Dala, Dawakin Tofa, Dawakin Kudu, Fagge, Gwale, Kano Municipal, Kumbotso, Kiru, Rano, and Gwarzo.
“A cikin mutane 100 da ake zargin an tabbatar da guda takwas, yayin da mu ke jiran karin sakamako.
“Mun rasa rayuka uku daga cikin takwas da aka tabbatar.”
Tsanyawa ya ce a halin yanzu majiyyata 27 su na karɓar magani yayin da 41 kuma aka sallame su.
Views: 37
