Yadda wasu ƴan Daba suka Sari wani Ɗalibin Jami’a akan Gardamar Ƙwallo a Jihar Bauchi

Yadda wasu ƴan Daba suka sari wani Ɗalibin Jami’a akan Gardamar Ƙwallo

Wasu da ake zargin ƴan daba ne sun sari wani ɗalibin jami’a a jihar Bauchi bayan gardamar ƙwallon ƙafa ta ɓarke a tsakaninsu.

Ɗaya daga cikin ƴan daban ne dai ya sari ɗalibin mai suna Safiyanu Adamu da wuƙaƙe har guda biyu a hannunsa
Ɗalibin yana can kwance a asibiti ana duba lafiyarsa biyo bayan wannan aika-aika da aka tafka masa a kan ƙwallon ƙafa.

Jihar Bauchi – Ƴan daba sun sari wani ɗalibi mai suna Safiyanu Adamu, na jami’ar Sa’adu Zungur, da ke a Gadau a jihar Bauchi bayan ɓarkewar gardamar ƙwallon ƙafa.

Jaridar Leadership ta kawo rahoto cewa, lamarin ya auku ne lokacin da ake wasan ƙwallo a tsakanin Green-White-Green House da GT House a ranar Asabar, inda ɗaya daga cikin ƴan daban ya caka masa wuƙa.

‘Yan daba sun sari dalibin jami’a a jihar Bauchi
Dalibin da aka sara kwance a gadon asibiti.

Ɗan daban dai ya cakawa ɗalibin wuƙa ne a wuyan hannunsa na dama bayan gardamar ta rikiɗe ta koma faɗa.

Ɗaliɓin yana kwance a asibiti
Safiyanu Adamu wanda yanzu haka ake duba lafiyarsa a babban asibitin tarayya da ke Azare, ya bayyana cewa ana cikin wasan wani da ake kira Lado yaje gida ya ɗauko wuƙaƙe biyu waɗanda ya sare shi da su a hannunsa.

Rahotanni sun nuna cewa ɗaliban da suka yi ta maza suka tsaya da sauran wasu mutane sun ceto shi inda suka garzaya da shi babban asibitin Gadau, domin duba lafiyarsa.

An ba Safiyanu kulawar farko a babban asibitin na Gadau kafin daga bisani aka wuce da shi zuwa babban asibitin tarayya na Azare domin ba shi cikakkiyar kulawa.

Lokacin da aka nemi jin ta bakin kakakin rundunar ƴan sandan jihar, SP Ahmed Wakili, ya bayyana cewa zai tuntuɓi DPO ɗin yankin kan lamarin kafin ya bayyanawa ƴan jarida halin da ake ciki.

Sai dai, wani ɗan sanda a Gadau ya bayyanawa ƴan jarida cewa suna bakin ƙoƙarinsu wajen yayyafawa lamarin ruwan sanyi kada ya rikiɗe zuwa rikici bayan ɗaliban sun fara shirin ɗaukar fansa.

https://apahausa.com.ng/video-ku-kalli-yadda-%c6%b4a%c6%b4an-hausawa-suka-lalace-zina-a-fili/

Ya ce ƙoƙarin na ƴan sanda ya haifar da ɗa mai ido domin zaman lafiya ya dawo a garin inda kowa ya ci gaba da gudanar da harkokinsa.

Views: 48

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *