Yau ake cika shekaru goma da kashe tsohon shugaban kasar Libya—Muhammad Gaddafi

Yau ake cika shekara 10 da yi wa Gaddafi kisan gilla

Ga rahoton sashin Hausa na BBC

Shekara goma kenan tun bayan da yan tawaye suka kashe tsohon Shugaban Libya Muammar Gaddafi yayin juyin juya halin da aka yi a kasar a 2011. Mutane kadan a cikin Libya da wasu da ke wajenta sun yi hasashen irin rikici da yakin da kasar za ta shiga idan Gaddafi ya bar mulkin kasar.

Wakiliyar BBC ta Arewacin Afrika Rana Jawad na Libya a lokacin da aka kashe Gaddafi kuma ta yi duba kan irin rikicin da kasar ta shiga tun bayan lokacin.

A bayyane, yan kasar Libya ba su fitowa domin su tuna da ranar mutuwar Kanal Gaddafi. Yadda yan tawaye suka yi masa kisar rashin imani a lokacin da ya yi kokarin guduwa wata alama ce ta wani hali da kasar ke shirin fadawa.

Cikin shekara goman da suka shude, an gudanar da zaben yan majalisar dokoki har sau biyu, wanda aka yi karo na biyu a 2014 ya ja kasar ta dare biyu, inda a bangare daya aka samu gwamnati a Benghazi da ke gabashin kasar sai kuma a Tripoli da ke yammacin kasar.

Yakin da masu adawa da juna a kasar ke yi ciki da wajen kasar ya kara raba kan kasar. A yau bayan shekarun da Majalisar Dinkin Duniya ta shafe tana shiga tsakanin bangarorin da ke rikici a kasar, da kuma irin matsin lamba da kasar ke samu daga sauran kasashe, ana sa ran Libyar za ta gudanar da wasu zabukan a Disamba mai zuwa – duk da cewa mutane kalilan ne ke da yakinin zaben zai gudana.

Yakin basasa da kuma irin rudanin da aka shiga na shekaru ba doka a kasar, ya sa aka fara mantawa da abin da aka fara tunanin wata sabuwar rayuwa za a shiga mai dadi bayan juyin juya halin da aka yi.

Sai dai a maimakon haka, farar hula ne suka yi ta gwagwarmaya da rayuwarsu domin su tsira a tsawon wadannan shekaru.

Amma duk da haka akwai sauran wasu yan Libyan da suka ci gaba da hankoron ganin lamura sun daidaita tare da samun yancin da aka yi zaton za a samu shekara goma da suka wuce bayan hambarar da Gaddafi.

Views: 100

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *