
Dan kasuwa ya kwace motar Kwamisshinan Gwamna Tambuwal saboda ya karbi bashin Buhun Shinkafa ya kasa biya~Sheikh Bello Yabo
Shahararren malamin addinin musulunci a jihar Sokoto Sheikh Bello Yabo tonawa wani Kwamisshinan Gwamna Tambuwal asiri bayan da ya karbi buhun Shinkafa a hannun wani dan kasuwa ya kasa biya.
Bello Yabo ya bayyana hakan ne a cikin wani wa’azi daya gabatar, wanda yake kira ga Gwamna Tambuwal daya ji tsoron Allah ya taimaki al’ummar jihar Sokoto daya jefa a cikin kangin talauci.
Malamin ya bayyana cewa tarihin jihar Sokoto ba a taba Gwamnan da ya cuci al’ummar jihar Sokoto kamar Gwamna Tambuwal ba.
Malamin ya ce yanzu hatta Kwamisshinansa cikin kuka su ke, domin yanzu akwai wani Kwamisshinan Gwamnan da aka kwacewa mota kirar PRADO ta gwamnati saboda bashin buhun Shinkafa daya karbo.
Sokoto Online
Views: 18
