Za a Yiwa shahararren Ɗan Daudu Nan Bobrisky Dashen Mahaifa A Ingila

DA ƊUMI ƊUMI: Za a Yiwa Ɗan Daudu Ɗin Nan Bobrisky Dashen Mahaifa A Ingila.

Labarin dake Sshigo mana yanzu ya tabbatar mana an samu nasarar yiwa rikàƙƙén Ɗan dàudú ɗin nan dake zaune a jihar legas wato Bobrisky tiyata a mazaunansa, dakuma al auwarsa, yanzu haka a ƙasar ingila.”

Rahoton ya tabbatar da cewa yanzu Bobrisky baida maraina sannan an ɗebe su gaba ɗaya sannan an kara masa girman mazaunansa, an kuma yi masa dashen nono a kirjin jinsa, abinda ya rage kawai shine za ai masa dashen mahaifa ta yadda zai iya samun ciki har yakai ga haihuwa.”

Jaridar ALFIJIR HAUSA ta tattaro cewa Bobrisky ya kashe maƙudan miliyoyin kuɗaɗe domin ganin an sauya masa duk wasu halittun jikinsa daga jinsin maza zuwa ta mata, “inda ya kara bayyana hakan a cikin wani bidiyonsa cewa a shirye yake ya ci gaba da ɓatar da maƙudan miliyoyin kuɗaɗe sama da waɗanda ya kashe a baya don ganin tabbatan an dasa masa mahaifa.”

Shin ko menene ra’ayoyinku kan wannan aikin na ƙarshe da za a yiwa Bobrisky ɗin ?

Views: 128

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *