Zan ba duk Namijin da ya Aureni, Gida, Mota da ₦50M amma da sharaɗi bazai min Kishiya ba
Wata matashiyar budurwa ta nuna muradinta na son shiga daga ciki sannan ta sanya garabasa a kai don jan hankalin yan maza.
Matashiyar ta yi alkwarin ba duk namijin da ya yi nasarar mallakarta gida mota, da kudi naira miliyan 20
Budurwar wacce ta ce tuni aka fara aika mata da sakonni ta ce sharadin auren shine ba za a yi mata kishiya ba.
Wata kyakkyawar budurwa yar arewa ta nuna aniyarta na son shiga daga ciki inda ta fito dandalin soshiyal midiya domin tallata kanta.
Domin karfafawa maza gwiwar neman aurenta, matashiyar ta yi alkawarin baiwa duk wanda ya yi nasarar samunta gida, mota da kuma kudi har naira miliyan 50.
Matashiyar budurwa na neman mijin aure amma bata son kishiya.
Zan Ba Duk Namijin Da Ya Aureni Gida, Mota Ma Miliyan 50 Amma Da Sharadin Ba Kishiya, Matashiyar Budurwa Hoto: @northern_blog Asali: Twitter
Duk wanda ya yi nasarar aurena ba zai yi mun kishiya ba, budurwa.
Sai dai kuma ta gindaya sharadi guda cewa duk namijin da ya aureta ba zai yi mata kishiya ba.
Har ila yau, a wata hira da aka yi da matashiyar domin tabbatar da ko da gaske take, ta jadadda maganar tata, inda ta ce tuni maza suka fara aiko da sakonni domin shiga sahun manemanta.
Ta kuma bayyana cewa zuwa nan da yan kwanaki za a gama tantance su sannan za a sanar da wanda ya yi nasara da zaran an kammala.
Ku Latsa wannan jan rubutun BIDIYON NAN
Views: 11
