Zan biya Mijina sadakin sa Idan har zai iya biya na gamsar dashi da nayi—Ta bayyana wa Kotu

  • Wani dan kasuwa mai suna Yahaya Mohammed ya fada ma kotu cewa zai yi wa matarsa sakin da ta nema idan ta biya shi N160,000 da ya kashe mata
  • Matar, Hauwa Hamza ta ce za ta biya kudin idan har mijinta Mohammed ya biya ta gamsar da shi da ta yi da kuma girkin da ta shafe shekaru tana yi masa a matsayin matarsa
  • Tun farko Hauwa ta tunkari wata kotun Kubwa inda ta nemi a raba aurensu mai shekaru uku saboda mijinta baya kula da ita kuma baya ganinta da gashi

Wata matar aure mai suna Hauwa Hamza ta tunkari wata babbar kotu a Kubwa, babban birnin tarayya, inda ta nemi a raba aurenta da mijinta, Yahaya Mohammed.

Hauwa ta nemi a raba aurensu ne kan cewa mijinta Mohammed baya bata kulawa kuma baya ganin mutuncinta.

Zan sake ki idan kika biya ni N160,000 da na kashe maki, miji ga matarsa a kotu

Sai dai kuma, mijin wanda ya kasance dan kasuwa ya sanar da kotun cewar zai saki matar tasa idan har za ta biya shi N160,000 da ya kashe mata, Daily Nigerian ta rahoto.

Views: 52

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *