Photon Wani Mai Siyar Da Albasa
Rahotanni daga jihar Sokoto, sun tabbatar da cewa Gobara ta jawo asarar miliyoyin kudade, a kasuwar yan Albasa da ke jihar wani rahoto ya bayyana cewa, “Gobara a kasuwar albasa a Ramin Kura da ke jihar Sakkwato ta yi sanadiyyar asarar miliyoyin nairori ga manoma”.
Yadda Albasar Ta lalace
Kawo wannan lokaci dai babu rahotan jikkata ko asarar rai a sanadiyyar ta shin wannan gobara, in banda asarar da ta jawo wa manoman albasar kamar yadda rahotanni suka nuna, jihar ta Sokoto dai ta sha fama da gobara a cikin kasuwannin jihar.
Ko a farkon shekarar nan ma saida gobara ta jawo asarar dubban miliyoyi a babbar kasuwar jihar. Muna fatan Allah ya kiyaye faruwar wannan al’amari a nan gaba ameen.
Views: 49
