
Wasu Rahotannin da muke samu wadanda suke karo da juna na cewa an bayar da belin Sheikh Abduljabbar yayi da wasu Rahotannin ke nuna ba’a bayar da belin nasa ba.
Sai dai rahoton BBC Hausa ya bayyana cewa.
A ranar Laraba ne Alkali Ibrahim Sarki Yola ya ɗage sauraron ƙarar bayan da aka yi zama na biyu tun fara shari’ar a birnin Kano.
Gwamnatin jihar Kano ce ta shigar da ƙarar Malam Abduljabbar kan zarginsa da yin kalaman ɓatanci ga Annabi SAW.
Lamarin ya jawo ce-ce-ku-ce sosai a faɗin ƙasar ba ma jihar Kano kaɗai ba.
Wakilinmu na Kano Khalifa Shehu Dokaji ya ce ya ga Abduljabbar Kabara ya rame a wannan zaman kotu na biyun da aka yi ranar Laraba.
Mai Shari’a Sarki Yola ya ce ya ɗage sauraron ƙarar ne saboda duk hujjojin da aka gabatar sun yi masa tsauri ya yanke hukunci nan take.
Ya ƙara da cewa akwai bukatar ya sake duba su, sannan ya san matsayar da zai ɗauka kan sabbin tuhume-tuhumen da gwamnati ta gabatar a zaman kotun na yau kan Sheikh Abduljabbar, ku kuma mafani da tuhume-tuhumen farko da aka gabatar.
Lauyoyin gwamnati sun buƙaci a ba su dama su karanto sabbin tuhume-tuhumen da suka je da su a kan Sheikh Abduljabbar, amma nasa lauyoyin suka soki hakan.
Lauyoyin Abduljabbar sun ƙalubalanci takardar sabbin tuhume-tuhumen da lauyoiyin gwamnati suka gabatar.
Views: 107

A bari a game shari’ar zargin da ake masa mana. In dai an kawo wasu sabbin tuhume-tuhume, neman dora masa laifi ne.