
Gidan rediyon Freedom Muryar jama’a ya bada rahoton cewa hukumar Hisbah ta jihar Kano ta bayyana dalilin da yasa bata kama yayan masu kudi ko masu milki inda tace tana yin da’awa da koyarwar a matakai daban daban saboda haka irin salon da ake yiwa gama garin mutane ba shi za a yiwa nantan mutane ba.
A cewar Dr. Aliyu Kibiya, mu yadda muke kallon abin idan akace shugaba yayi laifi ba zuwa ake ana fada da lasifika a masallaci ba, akwai wadanda za suje su isar da sakon Allah a wajen shugaba kuma dama Allah shi ke shiryarwa.
Saboda haka akwai irin da’awar da za’a yiwa manyan mutane akwai kuma irin wacce za a yiwa sauran gama gari.
Freedom ta tuntubi jagoror Huzba inda yace sun kama yayan masu kudi da dama kuma suna kan kamawa a ko wane lokaci.
Views: 29
