Kungiyar gamayyar kungiyoyin Arewa sun ce bar inyamurai su kafa kasarsu idan ana son zaman lafiya.
Gamayyar Kungiyoyin Arewacin Najeriya sun yi kira da babbar murya ga shugaban ƙasa Buhari da cewar cikin gaggawa ya bada dama ga Inyamurai su kafa kasar da suke ta hanƙoro akai ta Biyafira domin zaman lafiyar Najeriya.
Wannan bayani na kunshe ne a cikin wata takardar sanarwa wadda ta samu sanya hannun mai magana da yawun gamayyar kungiyoyin Abdul-Azeez Sulaiman kuma aka rarraba ta ga manema labarai.
Kungiyoyin sun cigaba da cewar tuni ba tun yau ba suka bayyana matsayin nasu na a amince Inyamurai su kafa kasar tasu ta Biyafira domin bayin Allan ‘yan Arewa su samu natsuwa da kwanciyar hankali daga farmakin da tsagerun Inyamurai ke kai musu a yankin Kudancin Najeriya.
Game da martanin da shugaban kasa ya mayar wa tsagerun na cewa zai yi maganin su nan bada dadewa ba, kungiyoyin Arewan sun ce kalaman Buhari akan wannan matsala abin takaici ne da ke nuna gazawa da raunin gwamnatin shi a fili.
“Mu ba tsoro ko fargaba bane ‘yan Arewa ke yi na kasar nan ta rabe, sai dai kawai natsalar da ake fuskanta a har kullum shine ɓangaren manyanmu da ke ta kalaman ayi hakuri a zauna ƙasa guda, wanda hakan ne ya haifar mana da raini har sashin Kudanci ke mana kallon ba a bakin komai muke ba suke barazanar a raba ƙasa, wanda kowa ya san wanda zai ji jiki idan aka rabar ƙasar”.
Ya kamata shugabannin mu su gane cewar hanya guda ta kaucewa barkewar yaƙin basasa a Najeriya shine abar Inyamurai su kafa kasar tasu ta Biyafira.
Kazalika kungiyoyin sun yi kira ga jama’ar Arewa da su zauna lafiya su kwantar hankalin su, sannan su goyi bayan Inyamurai su yi gaba su bar mana Najeriya su tafi Biyafirar su.
Kuma sannan mun zuba ido mu ga matakin da shugaban kasa zai dauka nan da kwanaki 30 domin kawo karshen tataburzar da Kungiyoyin Inyamurai suke haddasawa a kasar nan a kusan kullum.
Amma Ku me nenen mahangar Ku ?
Views: 14
