Kamar yadda kuka sani shafukan sada zumunta na zamani wato Social Media, suna haɗa zumunci mai ƙarfi a wani lokacin ma har ta kai ga ƙulla alaƙar aure a tsakanin saurayi da budurwa.
Wani ango mai suna Aminu da amaryarsa mai suna Yetunde, sun sanar da duniya yadda Allah ya hada su har soyayyar da suke ta kai su ga yin aure.
A wani hoto da Aminu ya wallafa a shafin sadarwa, ya nuna yadda soyayyar su ta fara, inda ya aikawa Yetunde sakon farko a shafin Twitter a shekarar 2018.
Muna fatan Allah ya basu zaman lafiya mai ɗorewa da zuri’a ta gari ameen.
Views: 17
