Matuƙar za a sake yin zaɓen gwamna a Kano APC faɗuwa za ta yi—Hon Sha’aban Sharaɗa

Wasu gaggan ‘yan jam’iyyar APC mai Mulki a Kano sun kai korefe-korafe ga shugaban jam’iyyar na rikon kwarwa, gwamna Mai Mala Buni dangane da abin da suka kira da neman yi wa jam’iyyar kanshin mutuwa a jihar.

A ranar Talata ne wasu ƙusoshin jam’iyyar ciki har da tsofoffin gwamnan jihar ta Kano, Malam Ibrahim Shekarau da Sanata Kabiru Gaya da ɗan majalisar dattijai Sanata Barau Jibrin da ɗan majalisar wakilai, Sha’aban Sharada da wasu manyan ƴaƴan jam’iyyar suka gudanar da taro inda suka yanke shawarar cewa dole ne shugabancin jam’iyyar APC ya taka wa Gwamna Ganduje birki kafin lamura su dagule.

Honorabul Sha’aban ya bayyana wa BBC cewa jam’iyyar ta APC a jihar Kano na ƙara nutsewa a ruwa shi ya sa suka ga ya dace su ɗauki mataki saboda gujewa alhaki.

“Mun faɗi abubuwa kamar uku – gaba ɗaya zaɓen da ake cewa an yi daga bangaren gwamnati na shugabannin jam’iyya daga kananan hukumomi da mazaba, mun yi watsi da shi kuma ba mu san shi ba.

Views: 21

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *