
Wasu dakarun ƙasar ta Afirka ta Yamma sun nemi a kori wasu manyan jami’an soja da kuma samar da ƙarin kayan aiki don yaƙar masu iƙirarin jihadi.
An jiyo harbe-harbe a kusa da fadar shugaban ƙasa da kuma wasu barikin soja ranar Lahadi da dare a Ouagadougou babban birnin ƙasar.
Sai dai gwamnati ta musanta labarin yunƙurin juyin mulki ko kuma cewa an kama shugaban ƙasar .
Rahotanni na cewa ana tsare da Shugaba Kabore ne a wani sansanin soja.
Kazalika, sojoji sun kewaye gidan talabijin na gwamnatin ƙasar.

Ɗaruruwan mutane ne suka fito zanga-zangar nuna goyon baya ga sojojin duk da dokar hana fita da aka saka, sannan suka dinga ƙona ofisoshin jam’iyya mai mulki.
Bidiyon da aka rika yadawa a babban birnin kasar ya nuna wasu motoci masu sulke – wadanda rahotanni suka ce na fadar shugaban kasa ne – dauke da harbe-harben bindiga kuma an bar su a kan toituna.
Wakilin BBC Simon Gongo da ke Ouagadougou ya ce birnin ya yi tsit. Sai dai sojoji sun kewaye gidan talbijin na kasar.
Views: 20
