Zamu fice daga APC matuƙa Buhari ya goyi bayan mai mala buni—El-rufai

Za mu fice daga jam’iyyar APC matukar Buhari bai gaggauta janye kalaman sa na nuna goyon bayan bangaren Gwamna Mai Mala Buni kan shugabancin jam’iyyar APC ba~Gwamna Nasiru El-Rufa’i.

Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru El-Rufa’i ya bayyana cewa baza su taba yarda da matakin da Buhari yake shirin dauka na dawo da Mai Buni kan kujerar shugabancin jam’iyyar APC ba.

El-Rufa’i ya ce lallai doli ne Gwamna Mai Mala Buni ya sauka daga wannan matsayi tare da barma Gwamnan Neja Sani Bello.

Gwamnan ya yi barazanar barin jam’iyyar matukar akace za a ci gaba da yin wannan rashin adalci.

Views: 11

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *