A safiyar ranar talata ne kafafen watsa labarai suka fara yaɗa rahotanni cewa Kamfanonin bada lamuni na duniya sun kama jirgin shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a birnin Washington DC.
Sakamakon bashin da ake bin ƙasar wanda kuma fadar gwamnatin ƙasar ta musanta hakan, wata sanarwa ta bayyana cewar jirgin shugaban ƙasar yana cikin ƙoshin lafiya babu abinda ya sa me shi.
Shugaban na Najeriya dai yanzu haka yana ƙasar Amurka inda yake halartar babban taron ƙolin ƙasashen Afrika da shugaba Joe Biden ke jagoranta.
Shugaban na Najeriya dai ya tafi ya bar ƙasar cike da cece kuce game da binciken da aka ce ya bawa wasu ƴan majalissar dokoki ƙasar su aiwatar kan gwamnan babban bankin ƙasar na CBN.
Ga rubutun malam Datti.
HON. GUDAJI KAZAURE YA FISU GASKIYA
Ga wasu takardu da suka tabbatar Maigirma Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya kafa Kwamitin da zasu binciki satar da ake zargin Gwamnan Babban Bankin Nigeria yayi tare da wasu manyan mukarraban Gwamnati, kuma cikin kwamitin akwai Hon. Gudaji Kazaure a matsayin Sakatare
Na kalli bidiyon hiran da jaridar Premium Times tayi da Hon Gudaji Kazaure, yace Maigirma Shugaban Kasa ya bawa kwamitin nasu karfin iko su dakatar da Gwamnan Babban Bankin Nigeria, su sa a kulleshi sannan a masa binciken kwakwaf.
Hon Gudaji Kazaure yace amma kwatsam sai suka ga shugaba Buhari ya sake nada Gwamnan Babban Bankin Nigeria wa’adi na biyu, Gudaji Kazaurs yace saboda ana cin amanar Buhari, yace Buhari idan kazo masa da batu ka rantse masa da Girman Allah to shikenan zai yadda da kai, yace yawanci abinda mukarraban Buhari suke kawo masa a takarda na karya ne yake hawa kai ya zauna ba tare da ya sani ba
Wato idan kun fahimta, tun kafin wa’adin farko na Gwamnan babban bankin Nigeria Godwin Emefiele ya kare aka gano yayi wannan satar, kuma Buhariya bada umarni a bincikeshi, amma sai wasu tsinannu da suke tare da Shugaba Buhari suka shiga suka fita suka shashantar da maganar har suka sa Buhari ya sake nadashi mukami wa’adi na biyu.
Hon. Gudaji Kazaure ya sadaukar da rayuwarsa ya fara musu fallasa, ance har kakakin Shugaban Kasa Garba Shehu yana daga cikin wadanda sukayi yunkurin karyata Hon Gudaji Kazaure, to ina ganin wannan shine dalilin da yasa Gudaji Kazaure ya fitar da wannan takardan, kuma tsinannu sun toshe duk wata hanyar da Gudaji Kazaure zai gana da Shugaba Buhari ya sanar dashi abinda yake faruwa
Gashi kuma sun saki makudan kudade sun bawa wasu tsinannun ‘yan jarida domin su lalata tasirin Hon. Gudaji Kazaure, manyan jaridu da kafofin watsa labarai da suke da tasiri sun basu kudade domin kar su yada maganganun Hon. Gudaji Kazaure
Gwamnan Babban Bankin Nigeria Godwin Emefiele to yana da masu gidansa a fadar shugaban kasa da Ministoci masu tasiri, duk harkallar da yakeyi sai da amincewarsu, tare suke komai, shiyasa suke bashi cikakken kariya har ya kawo wannan lokacin Buhari bai koreshi ba
Anyi satar dukiyar ‘yan Nigeria mafi muni a tarihi, da wannan kudi da aka sace Hon. Gudaji Kazaure yace bai kamata Nigeria ta ci bashi ba, ya dace ‘yan Nigeria mu cigaba da yada wannan batun, kuma ya kamata abi duk wata hanya na lumana a jawo hankalin Shugaba Buhari domin ya saurari rahoton Hon. Gudaji Kazaure
Muna rokon Allah Ya tona asirin duk wanda yake da hannu a wannan satar da akayi
Views: 13
