Tsohuwar uwar gidan tsohon shugaban Najeriya Goodluck Ebele Azikiwe Jonathan Patience Jonathan na mafarki sake komawa Villa wato fatar Shugaban Najeriya.
Domin kuwa wata jaridar turanci tace Patience Jonathan ɗin tace tana mafarkin mai gidanta Goodluck Jonathan ya sake zama shugaban ƙasa.
Patience Jonathan da mai gidanta Goodluck Ebele Azikiwe Jonathan dai sun bar faɗar Shugaban Najeriya ne a ranar 29-May-2015 bayan ra tsar da Shugaba Muhammadu Buhari wanda ya yi nasarar lashe babban zaben kasar da aka gudanar a 2015 ɗin
A wani labarin kuma
Mataimakin dan takarar shugabancin ƙasa na jam’iyyar APC, Kashim Shettima, ya sha alwashin tabbatar da cewa mawallafin jaridar DAILY NIGERIAN, Jaafar Jaafar da sauran ‘yan Najeriya da ke gudun hijira sun dawo gida idan jam’iyyarsa ta lashe zaben shugaban kasa a 2023.
Ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi lokacin da ya baƙunci shirin “Fashin Baki,” shirin Hausa na kai-tsaye na mako-mako, wanda Bulama Bukarti, Nasir Zango, Abba Hikima da Jaafar Jaafar ke gabatarwa.
A watan Oktoban 2018, wannan jaridar DAILY NIGERIAN ta buga faifan bidiyo na musamman da ke nuna gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje, na sanya wasu makudan kudaden daloli a aljihu, da ake kyautata zaton cin hanci ne daga ‘yan kwangilar da ke gudanar da ayyuka daban-daban da gwamnatin jihar ta bayar.
Daga baya gwamnan ya yi barazanar “saka kafar wando ɗaya” da ɗan jaridan, duk da ya shigar da Jaafar ɗin kara a wata babbar kotun birnin tarayya Abuja.
Jafaar, bayan an yi masa barazana ga rayuwarsa, ya gudu ya ɓuya kafin daga bisani ya koma kasar Birtaniya.
Sai dai, a shirin, Shettima, yayin da ya ke amsa wata tambaya kan halin da Jaafar ya shiga, ya ba da tabbacin cewa, Bola Tinubu shugaban kasa zai kare hakkin kowane ɗan Nijeriya tare da samar da yanayi mai kyau don gudanar da harkokinsu na halal.
“Jafaar abokina ne kuma amintacce, kuma ina ganin maganar za ta kare. Amma a tuna, ba Jaafar ne kaɗai ke gudun hijira ba; ko da dan uwana, Bulama Bukarti, ya na da dalilin barin kasar nan- ko da yake ba batun da za a tattauna a wannan fili ba ne.
“Abin da zan iya tabbatar muku, shi ne, za mu tabbatar da cewa, da yardar Allah, an warware dukkan al’amura domin mutanenmu su dawo gida,” in ji Shettima.
Views: 12
