Kamar dai yadda kuka sani ƴan mata da samari na baje kolinsu a shafukan sada zumunta na zamani wato Social Media.
Inda wasu ke amfani da kafafen na sada zumunta irin su Facebook, Twitter, Instagram, da dai sauransu wajen gudanar da harakokin da suka shafi kasuwanci.
Wasu kuma ke yin rubuce-rubuce da nufin jan hankalin mabiyansu wato followers, ta yadda za kuga ƴan mata da samari na yin abubuwan da zasu ɗauki hankulan abokansu na sada zumunta.
Yau muna ɗauke da rubutun wata matashiya mai suna Aisha ukey da tayi a shafin ta na Twitter inda tace “Mun shigo wata shekarar ba tare da miji ba Allah ka taimake mu” ga hoton Screenshot ɗin rubutunta nan daga ƙasa wanda tayi da harshen turancin Ingilishi.

A wani labarin kuma.
Gwamnatin Tarayya za ta mayar da tubabbun ƴan ta’adda 613 cikin al’umma don suvi gaba da rayuwa kamar sauran mutane.
Babban hafsan hafsoshin tsaron Nijeriya, CDS, Lucky Irabor, ya ce akalla ƴan ta’adda 613 da suka tuba masu karamin karfi za a mika su ga gwamnatocin jihohin su domin su koma cikin al’umma.
Irabor ya bayyana haka ne a jiya Alhamis a yayin taron masu ruwa da tsaki na Operation Safe Corridor, OPSC karo na biyar a Abuja.
CDS ɗin, wanda ya samu wakilcin babban jami’in horas da jami’an tsaro na kasa, Adeyemi Yekini, ya ce a halin yanzu, tubabbun ƴan ta’addan na ɗaukar horo kan cire musu tsattsauran ra’ayi da kuma canja musu tunani, ƙarƙashin OPSC.
A cewarsa, taron zai tattauna shirin cire tsatstsauran ra’ayi, canja tunani da kuma mayar da tubabbun ƴan ta’addan cikin al’umma.
Irabor ya ƙara da cewa, shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ne ya kafa kungiyar ta OPSC a watan Satumbar 2015 a matsayin wata dama ga ƴan ta’adda masu son su ajiye makamai su rungumi zaman lafiya.
Ya kara da cewa kuma haka kuma yana da kyau a bayyana cewa bayan kammala shirin, za a baiwa ko wannen su kayan abinci da kuma wasu kayayyakin amfanin kansa, da kuma kayan da zai fara sana’a, daidai da sana’ar da ya koya a lokacin horaswa ta yadda za su kafa kananan sana’o’i kuma su fara sabuwar rayuwa a cikin mutane.
Irabor ya bukaci gwamnatocin jihohin da ke karbar bakuncin su da su bayar da goyon bayan da ya dace don baiwa tsoffin mayakan damar manta wa da rayuwar ta’addanci gaba ɗaya.
Views: 24
