Abba Kabir Yusuf ya bayyana matakin da zai ɗauka a kan Aisha Bichi

A ƙarshen makon nan ne rahotanni suka karaɗe shafukan sada zumunta na zamani wato Social Media da labarin abinda ya faru tsakanin ɗan takarar gwamnan jihar Kano a ƙarƙashin jam’iyar NNPP Eng Abba Kabir Yusuf da mai ɗaki
Shugaban hukumar tsaro ta farin kaya DSS Aisha Bichi

Inda aka zargi Aisha da yunƙurin cin mutuncin Abba Kabir Yusuf har zuwa wannan lokaci dai a nashi ɓangare ɗan takarar gwamnan jihar ta Kano Abba Kabir Yusuf bai fito yace uffan game da wannan batu ba sai dai wasu daga cikin makusantansa sun ari bakinsa sun ci masa albasa inda suke ce.

Abban ba zai ɗauki matakin ramuwar gayya akan Aisha Bichi ba koda bayan ya zama gwamnan jihar Kano saboda shi mutum ne mai haƙuri da yafewa waɗanda suka ɓata masa.

A wani labarin kuma.

Gwamnatinn Nijeriya ta yi watsi da rahoton yiwuwar soke zaɓen 2023

A yau Talata ne gwamnatin tarayya ta baiwa ƴan Nijeriya tabbacin cewa zaɓukan 2023 za su gudana kamar yadda aka tsara.

Mai girma ministan yada labarai da al’adu, Lai Mohammed ne ya bayar da wannan tabbacin a Abuja a wajen taron nuna ƙoƙarin gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari daga 2015-2023.

Lai Mohammed ya na mai mayar da martani ne kan wani rahoto da aka yada, wanda jami’in hukumar zabe ta kasa INEC ya bayar, cewa zabukan 2023 na fuskantar babbar barazana ta soke wa saboda rashin tsaro.

Sai dai kuma ministan ya ce babu wani abin fargaba game da rahoton na bogi domin gwamnati ta tashi tsaye don tabbatar da an gudanar da zaben cikin lumana da aminci.

Mu a Matsayin Gwamnatin Tarayya shi ne cewa za a gudanar da zaben 2023 kamar yadda aka tsara. Babu wani abu da ya faru da ya canza wannan matsayi.

Kuma Muna sane da cewa INEC na hada kai da jami’an tsaro domin ganin an gudanar da zaben cikin nasara a fadin kasar nan.

Haka zalika Hukumomin tsaro sun kuma ci gaba da tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa suna bakin kokarinsu wajen ganin an gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali,” in ji ministan.

Views: 15

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *