Ƴan Najeriya 159 ne suka canza ƙasa a 2022

Gwamnatin Najeriya ta ce akalla ‘yan Najeriya 159 sun ajiye kasancewarsu ‘yan Najeriya kuma sun karbi zama ‘yan wasu kasashen na daban.

Babban sakatare a ma’aikatar cikin gida ta kasar, Dr Shuaib Belgore ne ya sanar da haka yayin wata ganawa da manema labarai da aka shirya a fadar shugaban Najeriya da ke Abuja.

Dr Belgore ya ce ‘yan Najeriya 150 ne suka sauya sheka tsakanin 2006 zuwa 2021.

A 2022 kuwa, ‘yan kasar 159 ne suka dauki irin wannan matakin. Sai dai ministan cikin gida Rauf Aregbesola, wanda shi ma ya halarci wannan ganawar, ya ce tudadar ‘yan kasar zuwa kasashen ketare ne ya haifar da karancin fasfuna da ake fama da shi a halin yanzu.

Ya kara da cewa a 2022 kawai, hukumar shige da fice ta Najeriya (NIS), ta samar da fasfo 1,899,683, wanda ba a taba samun haka a cikin shekara bakwai da ta gabata.

Ministan ya ce hukumar shige da ficen ta kuma samar da fasfuna fiye da miliyan 9 daga 2015 zuwa 2022.

Rahoton BBC Hausa

Views: 17

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *