Abubuwa 5 da zasu inganta mu’amalar auren ku a shimfida

Fahimtar wadannan abubuwa in sha Allah zai taimaka muku wajen inganta mu’amalar ku a shimfida.

1 :- Fahimtar me abokin zaman ka ke buqata. Wani alamu suke nunawa in suna buqatar s**, shin fada da masifa na rashi ko qarancin samun abun ne ? Fadanci da kyautatawan dan shimfidar saqon abunda ake buqata ne da dare ko in an dawo ? Ko dabi’ar sa/ta ne mabuqaci/ya ne, ko mai qarancin buqatane/ce, me suke son ayi musu na wasanni, etc. wannan zai taimaka muku wajen sanin abunda abokan zama ke buqata.

2 :- Sani da fahimtar me yasa ake buqata. Shin ya/ta dawo daga tafiyane, dabi’a ce, an kwana 2 ba’ayi bane, ta kusa ko ta gama period ne, kwanakin da suke iya juriya babu sun soma qurewa, magani suka sha ( dan qarin sha’awa ko neman haihuwa ko wani abu daya shafi nan). Fahimtar haka zai sa kusan yanayin da abokan zaman ku ke ciki.

3 :- Yaushe suke so. Fahimtar lokacin da abokin zama yafi samun nitsuwa da jin dadin ayi, shin farko ko tsakiyar dare ne, bayan sallah asubane ko da hantsi, bayan an dawo daga office/kasuwa, kafun period ko bayan period, sai yara sunyi bacci ko aun fita, etc. Fahimtar hakan yakan baku daman sanin lokacin da ayi ba tare da daya ya zo daya ya nuna ba yanzu ba.

4 :- A ina su kafi son ayi. Sanin inda abokin zama yafi samun nitsuwa da jin dadi yana taimakawa wajen basu damar sakewa ayi ba takura. Shin a daki ne, palour, kitchen, in da ba motsin masu wucewa, ko ba baby ko yara a daki. Sanin hakan yakan maku damar kebe wajajen da kukafi samun nitsuwa da sakewa lokacin mu’amala. Rashin sanin hakan kan iya jawo baudewa da rashin sake da jin dadi lokacin yi.

5 :- Yaya suke son ayi. Sani da fahimtar yaya abokin zama ke son ayi abun yana da muhimci sosai wajem samar da cikakken gamsuwa a tsakani. Sanin wasannin dake motsa musu sha’awa, yadda suke son ayi shin a hankali, da sauri, gaba ɗaya, da tallafin pillow ko ba buqatar haka, kalar kwanciya/ wajen kwanciya da ya ke samar musu da gamsuwa, ya suke son ayi musu in anayi, sau nawa suke son ayi, etc. Sanin wannan zai taimaka wajen samar ma juna cikakken gamsuwa.

Matuqar zaku karanci wadannan na abokan zaman ku in sha Allah zaku magance abubuwa da dama a wannan barayin, kuma zai rage muku ganin takura, cutarwa ko wahalarwa da kuke zargin juna dashi.

In fahimtar haka zai wahalar daku ku tambayi juna irin abubuwan da suke so,ya suke, yaushe suke, a ina suke so, tayaya suke, koface ta qara fahimtar juna.

source: sirrin riƙe miji facebook

Views: 36

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *