Idan aka sace ni kar wanda ya saki ya biya kudin fansa a sake ni—Ummi El-rufai

Mai dakin gwamnan jihar Kaduna Ummi ta bayyana cewa ko sace ta aka yi kar wanda ya kuskura ya bada kudin fansa domin a sako ta, sai dai wasu na ganin cewa wannan ikirari na mai dakin gwamnan jihar ta Kaduna, ba da gaske take ba.

Domin wasu na cewa da zarar ta shiga hannu za’a biya kudin fansar, idan ba’a manta ba a watannin da suka gabata ma saida gwamnan jihar ta Kaduna Malam Naseer Al’rufai saida ya ce ko iyalansa aka sace ba zai biya kudin fansa ba.

Najeriya dai na fama da tashe tashen hankula iri iri wadanda suka addabi kasar suka kuma hana ta cigaba kama daga rikice rikicen addini, kabilanci da satar mutane domin neman kudin fansa.

Nenene ra’ayoyinku a kai?

Views: 41

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *