Shugaba Buhari ya yi nasiha ga ‘yan kasuwa masu kara farashin kayan abinci a Ramadan
Shugaba Buhari na Najeriya ya gargadi ‘yan kasuwa masu kara farashin kayan abinci a watan Ramadan. Ya ce wannan dabi‘a ta yi hannun riga da addinin Islama.
Shugaban a cikin sanarwar da mai magana da yawunsa Garba Shehu ya fitar, ya ce, azumi bai takaita ga rashin cin abinci ba; ya kunshi kauce wa duk wani abu da ka iya cutar da dan Adam.
source dw hausa
Views: 20
