- Isa Ali Ibrahim Pantami ya yi jawabi a taro a kan muguwar illar yi wa shafukan yanar gizo kutse
- Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani na Najeriya ya ce ya zama dole a yaki wannan barna
- Pantami ya ce gwamnati kadai ba za ta iya magance matsalar ba, sai kowa ya bada gudumuwarsa
Abuja – Isa Ali Ibrahim Pantami wanda shi ne Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, ya koka kan yawaitar masu kutse a shafukan yanar gizo.
A ranar Talata, The Cable ta ce Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami ya gabatar da jawabi wajen wani taron kwana biyu na karawa juna sani da aka shirya.
Ma’aikatar sadarwa ta tarayya da hadin gwiwar babban bankin Duniya su ka shirya taron masu ruwa da tsaki wajen kare shafin yanar gizo a Abuja.
Mai girma Ministan yake cewa yayin da ake ganin cigaban fasaha a Duniya, ana samun masu yi wa shafukan gizo kutse kusan dare da rana a kullum.
Isa Ali Ibrahim Pantami ya koka
Kamar yadda jaridar ta fitar da rahoto a jiya, Isa Ibrahim Pantami ya nuna wannan danyen aiki ya zama cikas ga kamfanoni da kasuwanci a Duniya.
Bankin Duniya ya yi hasashen darajar tattalin arzikin zamanin Afrika zai kai $180b nan da 2025, hakan ya nuna za a samu damamaki da cigaba a nahiyar.
Domin a bada kariya aka fito da dabaru a 2022, har ta kai aka kafa hukumata musamman ta NDPB, amma Ministan ya ce gwamnati kadai ba za ta iya ba.
Canjin Gwamnati a Najeriya
An fara shirye-shiryen mika mulki a Najeriya, rahoto ya zo cewa kwamitin PTC ya karbi mutanen Bola Tinubu a matsayinsa na zababben shugaban Kasa.
Sakataren gwamnatin tarayya wanda shi ne shugaban PTC na kasa ya bada wannan sanarwa, ya ce Tinubu ya bada sunan Gwamnan Kebbi da Wale Edun.
source: legit.hausa.ng
Views: 22
