- Wani uba ya dauki wata matashiya mai kirkirar bidiyo aiki domin su gwada ko diyarsa na yin sharholiya a makaranta
- Ya boye a wajen da za a yi mata gwajin inda ya zuba ido yana kallo yayin da aka baiwa diyarsa damar kwana da wani kan kudi N300k
- Abun da ya faru a gaba ya tsuma zukatan mutane da dama yayin da mutumin ya fito daga inda ya boye sannan ya baiwa diyar tasa mamaki
Wani dan Najeriya ya baiwa diyarsa tukwicin kudi da sauran abubuwan karfafa gwiwa bayan ya yi mata gwajin kwanciya da wani kan N300k.
Da yake zantawa da Shuga Plum, wata mai ai kirkirar bidiyo kafin gwajin, mutumin ya ce ya ga yadda maza ke daukar kananan yara don haka yake son tabbatar da irin rayuwar da diyarsa ke yi a makaranta.
Ya isa wajen gwajin sannan ya nemi wuri ya boye. Ga farin cikinsa, diyarsa mai suna Chidinma, ta isa wajen, ta ki amsa tayin sannan ta bayyana cewa ita bata taba tarawa da wani ‘da namiji ba.
Uban wanda ya cika da alfahari ya fito daga wajen da ya boye sannan ya jinjinawa diyar tasa cikin daga murya.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
A nan take, ya baiwa matashiyar kyautar miliyan daya, ya yi mata alkawarin mayar da ita Canada da mota. Uba da diyar tasa suka rungume junansu yayin da suke farin ciki.
Bidiyon na TikTok ya haddasa cece-kuce a tsakanin masu amfani da soshiyal midiya.
Kalli bidiyon a kasa:
Views: 22
