“BIDIYO:” Yadda Ango ya hau Tsani domin ya Sumbaci Amaryar shi saboda tsawon shi bai kai ba

  • Wata yar dirama ta afku a yayin wani bikin aure lokacin da angon ya hau saman tsani don sumbatar amaryarsa bayan an daura masu aure
  • Mutumin ba gajere bane chan, amma dai matar ta fi shi tsawo sosai hakan ya sa aka kawo tsanin
  • Surukinsa ne ya haifar da abun ban dariyar domin dai shine ya hawo da tsanin kan mumbarin

Wani bidiyon ban dariya a TikTok ya nuno lokacin da wani mutum ya hau saman tsani don ya sumbaci matarsa a wajen daurin aurensu.

A bidiyon wanda @swagmotive ya wallafa, an kawo tsanin ne domin mutumin ya samu damar isa ga matarsa sannan ya sumbaceta da kyau.

Ango da amarya cikin shauki
Ango Ya ‘Dare Saman Tsani Don Tsawonsa Ya Kai Kuncin Amaryarsa a Bidiyo Hoto: @swagmotive. Asali: TikTok

A zahirin gaskiya ba wai mutumin na da gajarta sosai bane illa dai matarsa ta fi shi tsawo sosai.

Kara karanta wannan

Bidiyo ya nuno ango tsaye kan tsani a gaban amaryarsa

Da ace bai hau tsanin ba, zai iya sumbatar amaryar tasa. Surukinsa ne ya haddasa yar diramar mai ban dariya.

Ana gama ayyana mutumin da amaryar tasa a matsayin mata da miji, sai surukinsa ya gaggauta hawa mumbari da dan karamin tsanin a hannunsa.

Gaba daya wajen ya kaure da dariyar jama’a da ke cike da farin ciki yayin da mutumin mai tsananin biyayya ya haye saman tsanin kuma nan take tsawonsa ya karu sannan uya sumbaci matar tasa.

Bidiyon ya yadu sannan ya ja hankalin mutum fiye da miliyan 5 da suka kalle shi a TikTok yayin da mutane suka bayyana iyalin a matsayin masu farin ciki.

Kalli bidiyon a  @swagmotive

Views: 8

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *