LABARI DA DUMI DUMI: Kwankwaso ya mayar da martani kan taka hotonsa da Ganduje yayi

Hoton da ya jawo ce-ce-ku-ce a fagen siyasar Kano

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma tsohon sanatan Kano ta tsakiya injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso ya mayar da martani dangane ta zargin taka hotonsa da gwamna mai ci Dr, Abdullahi Umar Gabduje yayi a farkon makonnan da muke ciki inda yace.

“Ban cika son yin magana akan abinda ya shafi yaranmu na siyasa ko gwamnatin jihar Kano ba, saboda kowa daga cikinsu so yake ya zama kamar ni, duk wanda zaka tambaya a cikinsu so yake ya samu daukaka kamar yadda na samu, saboda ba wani abun tayar da jijiyoyin wuya neba ni a guri na” in ji shi.

Kwankwason dai ya kaucewa bada amsa akan tambayar da aka yi masa lokacin da yake zantawa da manema labarai, tun bayan raba gari tsakaninsa da gwamna mai ci Dr, Abdullahi Umar Ganduje aka fara samun takun saka tsakanin magoya bayansa da bangaren gwamnatin jihar.

Views: 14

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *