An shawarci shugaban EFCC da yayi murabus

Shugaban Hukumar EFCC Mr, Bawa

A ranar talatar da ta gabata ne shugaban hukumar da ke yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa ta’annati a Najeriya, ta EFCC, wato Abdulrashid Bawa ya sanar wa da duniya cewa ana yunkurin hallaka shi, dalilin da ya jawo maida martani daga sassa daban daban na kasar inda wasu ke zargin cewa masu mugun halin sata ne suke son ganin bawan Abdulrashid Bawa din.

Wasu yan Najeriya dai na ganin cewa ya sauka daga mukaminsa domin tsira da rayuwarsa yayin da wasu ke bayyana cewa, batun yayi murabus ma kwata kwata bata taso ba domin aikin bautawa kasarsa yake yi kuma duk dan kasa na gari ya kamata ya sadaukar da rayuwarsa koda zai mutu wajen kare girma da martabar kasar sa.

Shugaban na EFCC dai Abdulrashid Bawa, a nashi bangare ya ce babu gudu babu ja da baya har sai yaga abinda ya turewa Buzu nadin, inda ya ce batun yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya, yanzu aka fara, abinda kawai yake bukata shine addu’a da kuma goyon bayan yan kasa domin cimma nasara.

Kunji fa menene ra’ayoyinku shin kuna ganin ya kamata ya sauka ko kuwa yaci gaba da aikinsa?

Views: 10

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *