Yar gidan Zakzaky ta bayyana abinda ya faru da mahaifinta

Yar’ Gidan jagoran darikar Shi’a Sheikh Ibrahim Elzakzaky, Suhailat Elzakzaky a karo Na biyu.

Yar gidan Zakzaki tace har cikin dakin mahaifina yana sujada Sojojin Najeriya suka shiga suka bude masa wuta.”

Tace Mamata Zinatu tana ganin haka ta tashi ta Sha gaban Baba Na don kare harbin da Sojojin Najeriya suke masa, haka itama suka bude mata wuta sukai mata harbin fitar rai.”

“Ni Suhaila naga bala’i da masifa a wannan ranar, inata kiran mataimaka amma babu mai jina saboda a lokacin duk an kashe mataimakan.”

“Inaji ina gani aka kashe Dan uwana Ali Haidar, INA gani aka kashe Dan uwana Hammed, ni Suhaila ya zanyi da raina nayi kira ko zan sami mataimaki sainaji Gidan mu Gidan mu shiru bamai amsamin ga Abbana kwance cikin jini, ga mamata kwance cikin jini, ya Allah kana gani.” __ Inji Suhaila Yar Gidan Sheikh Ezakzky.

Views: 12

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *