Bana goyon bayan mulki ya sake dawowa Arewa a 2023— Shekarau

Sanata Ibrahim Shekarau

Mai girma tsohon gwamnan jihar Kano kuma sanata mai wakiktar shiyyar Kano ta tsakiya a zauren Majalissar dattijan tarayya Najeriya, Sanata Malam Ibrahim Shekarau ya bayyana cewa baya goyon bayan a sake bawa yankin arewacin kasar mulki a kakar zaben 2023 inda ya ce ya kamata mukki ya koma yankin kudancin kasar, domin samun dai dai to.

“A zahirin gaskiya ya kamata ace mulkin kasar nan ya koma yankin Kudancin Najeriya saboda a samu zaman lafiya da kuma dai daito a kasar nan duk da cewa tsarin karba karba ba tsari ne wanda kundin tsarin mulkin Najeriya ya kawo ba, amma dai tsarin yana da kyau kuma ya kamata ayi amfani da shi” in ji Malam Shekarau.

Malamin dai ya bayyana haka ne a zantawarsa da kafar yada labaran BBC, menene ra’ayoyinku dangane da wannan batu?

Views: 44

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *