
Hausawa sunce Mata adon gari wata matsala da take kunno kai tsakanin masoya ita ce rashin sanin abubuwan da suke raba soyayya domin da ace masoya sun san abubuwan da suke saurin raba soyayya ds sun kiyaye su amma a halin yanzu za mu dan kawo kadan daga cikinsu.
- Na farko akwai karya: ita karya wata abu ce mai yanke soyayya saboda idan saurayi ko budurwa daya ya rika yiwa daya karya musamman karyar kudi ko wani abun duniya, daga baya ya gano ko ta gano makaryaci ne to babu inda soyayyar zata je.
- Na buyu akwai rashin kulawa: kulawa kusan za ace ita ce jigo a fagen soyayya domin wasu na yi mata kirari da cewa duk girman soyayya rashin kulawa yana iya rusa ta.
- Sannan Akwai zargi,: shima yana daya daga cikin abubuwan da suke lalata zamantakewa koda ta aure ce balle ta masoya.
Views: 135
