Mace ko matarka ce ita ke da ‘yancin ta zaɓi lokacin da take da ra’ayin ka kwanta da ita—Samira Isah

Ku latsa nan don kallon Bidiyon nan

Wata matashiya kuma yar gwagwarmayar kwatar wa mata yancinsu a tarayyar Najeriya Samira Isa ta bayyana cewa ita a ra’ayinta ko miji bai kamata ya kwanta da matarsa irin kwanciyar saduwa tsakanin mata da miji ba ba tare da son ran taba ba.

A RA’AYIN NA: Mace ko matar aure ce ita ke da ‘yancin ta zaɓi lokacin da take da ra’ayin ka kwanta da ita, idan bata so ka kyale ta, sannan tana da damar zaɓar lokacin da take son ɗaukar ciki ko akasin haka, sannan uwa uba kuma ita ke da hurumin zaɓar tayi tsarin iyali ko ta cigaba da haihuwa. Ba wani zancen kai mijinta ne zaka yi mata yadda kake so. Domin jikinta ne ba naka ba!.

Duk wanda yake da ja ya fito ya yi bayani.

Inji yar Gwagwarmaya Samira Isa Modibbo kamar yadda shafukan Manuniya da Idon Mikiya suka ruwaito

Manuniya

Views: 455

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *