Amfanin da Ƙwaƙwalwa ke samu daga Baccin Rana

Amfanin da Ƙwaƙwalwa ke samu daga Baccin Rana

Masana sun bayar da shawarar yin barcin rana na ƙasa rabin sa’a a kullum.


Samun ɗan lokaci don rintsawa a kai-a kai, yana da matuƙar alfanu ga lafiyar ƙwaƙwalwa kuma yana taimaka wa bunƙasar ƙwaƙwalwa tsawon lokaci, a cewar masu bincike daga Jami’ar University College London.

Rukunin masanan ya nuna cewa ƙwaƙwalwar masu taɓa ƙailula ko barcin rana tana kan ma’aunin kyubik sentimita 15, daidai da matakin da za ta iya rage tsufa da kusan shekara uku zuwa shida.

Sai dai kuma, masana kimiyyar sun bayar da shawarar cewar barcin, kada ya kai na rabin sa’a.

A cewar ƙwararrun, barcin rana yana matuƙar wahala ga ma’aikata a fannonin sana’o’i da dama, inda a wasu wuraren aikin ake ganin baiken masu taɓa ƙailula.

“Muna ba da shawara cewa kowa ne mutum zai iya samun amfani daga barcin,” kamar yadda Dakta Victoria Garfield ta faɗa.

Ta bayyana sakamakon da aka gano da cewa “sabo ne fil kuma mai matuƙar ƙayatarwa”.

Barcin rana, muhimmin abu ne ga bunƙasar rayuwar ɗan’Adam a lokacin da muke jarirai, sai dai muna girma, yana daɗa raguwa amma yakan sake ƙaruwa a lokacin da muka yi ritaya daga aiki, an ba da rahoton cewa kashi 27 cikin ɗari na mutanen da suka haura shekara 65 suna gyangyaɗawa da rana.

Dakta Garfield ta ce shawarar yin barcin rana “aba ce mai matuƙar sauƙi” idan aka kwatanta da rage kiba ko kuma motsa jika wadanda ke da “wahala a wajen galibin mutane”.

Kaifin ƙwaƙwalwa bisa tsarin rayuwa yana disashewa yayin da shekaru ke ƙaruwa, amma shin ko barci yana taimakawa wajen yin kandagarkin cutuka kamar susucewar tunani, wannan wani abu ne da har yanzu yake buƙatar ƙarin bincike.

Lafiyar kwakwalwa tana da matuƙar muhimmanci wajen ba da kariya ga cutar tsananin mantuwa kuma larurar tana da alaka da katsewar barci.

Masana sun ba da shawarar cewa rashin isasshen barci yana lalata ƙwaƙwalwa a tsawon lokaci, kuma yana haddasa zogi sannan yana shafar jijiyoyin sadarwa tsakanin ƙwayoyin halittar jiki.

“Don haka, gyangyaɗi lokaci-lokaci yana iya kare mutum daga larurar mantuwa ko daina aikin ƙwayoyin halittun jijiyoyin laka ta hanyar rama tauyewar barcin da aka samu da dare,” a cewar jami’ar bincike Valentina Paz.

Sai dai Dakta Garfield na da ra’ayin cewa maimakon ta samu wuri mai taushi ta kwanta ta yi ƙailula gwamma ta motsa jiki tsawon minti 30, amma ta ce za ta iya bai wa mahaifiyarta shawarar ta yi irin wannan barcin.

Views: 60

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *