An Tsinci Tsohon Nan A Taraba Shekaru 60 Kenan Da Ɓacewarsa Yace A Zariya Yake
“Wani bawan Allah mai suna Mal. Idris Halidu haifaffen jihar Taraba in da ya bayyana cewa ya haɗu da wannan tsohon bayan yi masa wasu ƴan tambayoyi ya tabbatar masa cewa shi haifaffen birnin Zariya jihar Kaduna ne.”
“Mutumin daya tsincesa ya tabbatarwa da majiyarmu cewa shekaru masu yawa kenan tsohon yana gararanba a Jihar Taraba, kuma tsohon ya furta da bakinsa shekaru 60 rigis rabonsa da mahaifarsa kamar yadda majiyar Jaridar ALFIJIR HAUSA ta samu tabbacin hakan da safiyar Lahadi 2/07/2023.
“Tsohon ya ci gaba da bayyana cewa sunansa Abdullahi, sunan babansa Mal. Garba, cikin ƴan ƙannensa zai iya tunawa da Haruna, Sa’idu, Zainabu, ya kuma bayyana sunan anguwarsu da Anguwar Alƙali dake cikin birnin Zariya jihar Kaduna.”
“Idan Allah yasa ƴan uwansa za su iya ganesa tom su tuntuba waɗannan lambobin domin tattauanwa da waɗanda tsohon yake hannunsu a jihar Taraba.”
08038900854, 07056607383, 07012155310.
Allah yasa a dace Amin Summa Aminnn.
Views: 13
