Labarin yadda Maimunatu ƴar shekara 21 ta kashe mijinta da Wuƙa a jihar Bauchi

MATAR DA TA KÀSHE MIJINTA

Matar da ta kashé mijinta a Bauchi sunanta
Maimunatu Sulaiman ‘yar Shekara 21, sunan mijinta Aliyu Muhammad.

Kamar yadda ta bayyana wa ‘yan sanda masu bincike, tace cacar baki ne ya shiga tsakaninta da mijinta, sai da ta bari sun kwanta a kan gadonsu na Sunnah da nufin zasuyi bacci bayan kammala cacar bakin, sai ta dauko wuka ta caka masa a kirjinsa wanda hakan yayi ajalinsa.

Yanzu haka tana nan a sashin binciken manyan laifuka na ‘yan sanda State CID Bauchi, idan an kammala hada bincike za’a gurfanar da ita a Kotu

Muna fatan Allah Ya jikan Aliyu

Datti Assalafy

Views: 27

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *