Labarin yadda wata Mata da ta Haifi ƴaƴa 11 daban-daban duk Makafi
Wani faifan bidiyon wata mata ya yadu inda ta bayyana yadda ta haifi yara 11 dukkansu makafi.
Matar mai suna Agnes Nespondi ta ce dukkan yaran a haka ta haifesu gaba daya tun farko.
Ta ce lokacin da ta haifi yaronta na farko ta yi tunanin sauran ba haka za su zo ba kamar na farkon
Wata mata ta bayyana yadda ta haifi yara 11 dukkansu makafi a kafar sadarwa ta zamani, ta ce ita ta ke kula da su.
A wani faifan bidiyo da AfrimaxTV ta wallafa, matar mai suna Agnes Nespondi ta ce ta haifi yaran tun daga haihuwar su makafi.
Matar da ta haifi yara makafi 11, ta ce ita ta ke kula da su
Uwar Yara Makafi 11 Ta Bayyana Halin Da Ta Ke Ciki. Hoto: AfrimaxTV. Asali: Youtube.
Ta bayyana yadda ta haifi jaririnta na farko makaho, inda daga bisani ta haifo sauran 10 duka makafi.
Ta ce bayan ta haifi biyu makafi, ta yi addu’an samun masu ido a gaba don su kula da guda biyun da ba sa gani.
Dukkan makafin ‘ya’yan nata sun girma, sai dai guda biyu ‘yan kanana na karshe.
‘Ya’yan nata dukkansu sun girma, sai dai guda biyu na karshe su ne kawai ‘yan kanana a cikin yaranta, cewar Legit.ng.
A cikin hotunan da ta wallafa, ta nuna yadda ta ke son yaran nata wadanda ba za su iya taimakon kansu ba.
Ta bayyana yadda ta ke ji a rayuwa kamar tafi kowa rashin sa’a a duniya saoboda wannan jarabawa.
Views: 65
