Yadda Wani Fasto ya Mutu Sa’o’i kaɗan da shiga ɗakin Otal shida Budurwar sa

Wani Fasto ya Mutu Sa’o’i kaɗan da shiga ɗakin Otal shida Budurwar sa

Wani faston ɗariƙar Katolika ya yi bankwana da duniya bayan ya je otal cin duniya da tsinke tare da masoyiyar sa.

Fasto Joseph Kariuki Wanjiku mai shekara 43 a duniya ya kama ɗaki ne a otal ɗin da yammacin ranar Juma’a.

Sai dai, faston ya mutu ne da safiyar ranar Asabar bayan ya kwashe wasu sa’o’i a otal ɗin tare da budurwarsa

Nairobi, Kenya – Wani faston ɗariƙar Katolika mai shekara 43 a duniya ya mutu sa’o’i kaɗan bayan shi da masoyiyarsa sun je otal.

Jaridar The Punch tace faston mai suna Joseph Kariuki Wanjiku na cocin St. Peters Ruai, yaje otal ɗin Monalisa Hotel Delview a Gatanga tare da masoyiyarsa mai suna Ruth Nduhi mai shekara 32 da yammacin ranar Juma’a.

Fasto ya mutu bayan ya je otal da budurwarsa
Faston ya ce ga garin ku nan sa’o’i kadan bayan yaje otal Hoto: Punchng.com Asali: UGC


A cewar rahoton ƴan sanda budurwar ta gayawa shugabannin otal ɗin da safiyar ranar Asabar cewa faston yana ganin jiri inda yake fita hayyacinsa

Views: 20

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *