YANZU-YANZU: Shugaban Kasa Bola Tinubu Ya Ayyana Dokar Ta-baci Kan Farashin Abinci Da Kuma Bawa Manoma Tsaro

Daga Comr Abba Sani Pantami
Tinubu ya kuma bayar da umarnin a gaggauta sakin takin zamani da hatsi ga manoma da magidanta domin a dakile illolin cire tallafin man fetur.
Ya kuma umurci hukumar kula da kayayyakin abinci ta kasa da ta tantance farashin abinci tare da kula da dabarun tanadin abinci wanda za a yi amfani da shi azaman hanyar daidaita farashin hatsi da sauran kayan abinci. Ta wannan kwamitin gwamnati za ta daidaita hauhawar farashin kayan abinci a Najeriya.
Haka zalika yasha alwashin kare gonaki da manoma ta yadda manoma za su koma gonaki ba tare da fargabar hare-hare ba.
Mai magana da yawun shugaban kasa Dele Alake, shine ya bayyana hakan ga manema labarai a yau Alhamis.
Matukar Gwamnatin kasar ta gudanar da wannan aikin, na tabbata za’a samu saukin tsadar kayan masarufi da sauran abubuwan more rayuwa.
Views: 30
