Ƙarancin Samari yasa na dawo gida daga Amurka domin na ɗauki Saurayi na—Deenayaah

Ƙarancin Samari yasa Budurwa ƴar Najeriya dake Amurka dawowa gida ta ɗauki Saurayin ta

Wata ‘yar Najeriya da ke zaune a kasar Amurka ta dawo gida don tafiya da saurayinta zuwa can.

An ce budurwar ta dawo ne domin tafiya da saurayinta da ta bari a Najeriya saboda ta gaza samun nagartaccen saurayi a can.

Bayanai sun nuna cewa dama saurayin ya shafe sama da shekaru uku ba tare da aikin yi ba a daidai lokacin da masoyiyar tasa ta zo masa da wannan albishir

Wata ‘yar Najeriya da ke zaune a kasar Amurka, ta dawo Najeriya domin tafiya da saurayinta zuwa can.

Budurwar ta bar saurayin nata a Najeriya a lokacin da ta koma Amurka, amma bayan da ta samu duniya, sai ta yanke shawarar dawowa domin tafiya da shi.

Wata mai suna @deenayaah, wacce kawa ce a wurin wannan budurwa, ta wallafa wannan labarin a shafinta na Tuwita.

‘Yar Najeriya ta dawo ta dauke saurayinta zuwa kasar Amurka saboda rashin samun nagartaccen namiji.

An ce saurayin ya kasance yana ta fama da rayuwa ba tare da aikin yi ban a tsawon shekaru uku gabanin dawowar budurwar tasa daga Amurka.

Ta koka kan cewa babu nagartattun mazaje a Amurka
Deenayah ta ce dalilin da ya sa kawarta ta dawo ta tafi da saurayin nata shi ne saboda babu mazaje masu nagarta a inda take da zama, inda ta yi nuni da cewa yana da kyau a rika daraja mazajen Najeriya.

Ta ce mazajen Najeriya na daga cikin mafiya nagarta a duk duniya, a saboda haka ya zama dole a rika daraja su.

Views: 16

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *