Bokaye sun amsa kiran gwamnan Oyo

Gwamna Seyi Makinde

Rahotanni daga jihar Oyo da ke yankin kudu maso yammacin tarayyar Najeriya na cewa bokayen jihar sun amsa kiran da gwamna Seyi Makinde na jihar ya yi musu na cewa su fito suyi addu’a domin a samu maganin matsalolin da ke addabar jihar.

A jiya ne dai gwamnan jihar ta Oyo Mr, Seyi Makinde ya nemi bokaye da yan borin jihar ta Oyo da su fito suyi aiki irin wanda suka saba yi domin samun mafita daga matsalolin da ke addabar jihar.

Sai gashi a ranar Juma’ar nan an soma ganin Bokayen suna yin ayyukan su na tsubbace-tsubbace ta hawan bori domin neman samun waraka daga matsalolin jihar.

Jihar ta Oyo dai ta jima tana fama da matsalolin tsaro musamman fashi da makami da satar mutane domin biyan kudin fansa da sauransu.

Menene ra’ayinku?

Views: 16

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *