Kotu ta yanke hukunci kan zaɓen 2023—Akwai kura-kurai a zaɓen in jita

Kotu ta kori ƙarar Peter Obi na LP

Kada ma’aunin gaskiyarka ya zama don wane ya faɗa, ka ƙaryata masani a fanninsa, don ƙiyayya; kana kuma gaskata mai shaci-faɗi don soyayya. Wannan toshewar zuciya ce ga neman gaskiya.

Ɗauko darasin tarbiyya cikin hadisin Abdulllah ibn Ubayy ibn Ka’b da Shaiɗan ya karantar da babansa Ubayy ibn Ka’b رضي الله عنهما falalar Ayatul Kursiy, wacce tarbiyya za mu samu? Manzon Rahama ﷺ ce masa ya yi, abin da Shaiɗan ya faɗa gaskiya ne (صدق الخبيث) daban da halinsa. Shaiɗan ma kenan, ka ajiye batun yana ɓatar da mutane, ka KALLI GASKIYAR (Hakim, 2108).

Indai masani ya yi magana a fanninsa, ka saurara, ka nemawa kanka mafita, wannan shi ne reality. Ɗauko ‘fiƙhu’ cikin fassarar mafarkin Annabi Yusuf عليه السلام, Suratu Yusuf aya ta 43 zuwa ta 50, ya ce abin da yake zahiri gaskiya, za a yi wahalar abinci, don haka a yi tanadi, ba fatan tsiya ba ne, reality ne.

Sunusi dai masanin tattali ne na buga misali, ya riƙe CBN Governor daga 2009 zuwa 2014, ba da shaci-faɗi ya yi magana ba, da ilimi da tajriba ne. Wahalar nan kuma ana cikinta a zahiri, har jariran da aka haifa yau sun sani. Saboda tsanani NLC ta shiga yajin aiki jiya da yau, wannan duk ZAHIRI ne.

Maimakon ƙorafi, a nemi mafita kawai. Ka kuma zama mai buɗaɗɗiyyar zuciya kan al’amura, kar son zuciya ya rufe ma ido ka kasa gane gaskiya saboda shaksiyyar wani.

Views: 11

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *