Ɗan ƙwallon Duniya Christiano Ronaldo yace addinin Musulunci na birge shi

Gwamnan jihar Jigawa Malam Umar Namadi, yayi murnar zagayowar watan haihuwar fiyayyen Halitta Annabi Muhammad (S.A.W.).
A cikin wani sako mai ratsa zuciya, Mai Girma Gwamna Mallam Umar Namadi yana mika gaisuwa da taya murna ga al’ummar Jigawa da musulman duniya dangane da Mauludin Manzon Allah (SAW).
A cikin sakon nasa, Gwamna Malam Umar Namadi, ya yi tsokaci kan muhimmancin wannan lokaci mai albarka, wanda ke tunawa da haihuwar fiyayyen halitta Annabi Muhammad (S.A.W.) “Haskakar haske da kuma siffar rahama ga dukkan bil’adama”.
“Rayuwar Annabi Muhammad (S.A.W.) ta zama abin koyi ga dukkannin al’ummar duniya baki daya. Koyarwarsa ta tausayi, tawali’u, adalci, da kuma gaskiya mai ƙarfi ta ci gaba da yi mana ja-gora a rayuwarmu ta yau da kullum. Rana ce ta tunawa da muhimmancin bin kyawawan halayensa da koyi da kyawawan dabi’unsa in ji shi.
Gwamnan yana kwadaitar da kowa da kowa da su samu kwarin gwiwa daga rayuwar Manzon Allah da koyarwarsa, musamman ta fuskar kalubale da rashin tabbas a duniya. Ya yi kira da a yi amfani da dabi’un soyayya, juriya, da fahimtar juna don gina al’umma.
Gwamna Mallam Umar Namadi ya yi kira ga al’ummar jihar Jigawa, da a sake sabunta kudurin hadin kai da aka san jihar da su. Yana kira ga jama’a da su hada kai domin daukaka juna, tallafawa mabukata, tare da gina kyakkyawar makoma ga al’ummominsu.
Gwamna Namadi ya kammala sakonsa da addu’o’in samun zaman lafiya da farin ciki da albarka ga kowa da kowa da kuma tunatar da mu bin tafarkin Annabi Muhammad (S.A.W.).
“Allah ya sa wannan Mauludin ya kawo mana zaman lafiya, annashuwa, da albarka. Ya tunatar da mu aikin da ya rataya a wuyanmu mu yi koyi da tafarkin Annabi Muhammad (S.A.W.) da yunƙurin zama nagartattu a cikin al’umma.”
Hamisu Mohammed Gumel,
Babban Sakataren Yada Labarai na Gwamnan Jihar Jigawa.
Satumba 27, 2023.
Views: 35
