Magidanci ya kai maƙwafcinsa ƙara saboda ya satar masa dafaffen abinci ya ba ƴaƴansa

Alkali a garin dirin daji a jahar kebbi ya yankama mutumin da yakai karar makwafcinsa tarar biyan wanda yakai kara dubu talatin saboda ya debi dafaffen abincin gidansa ya ciyarda yayansa takwas da sukayi kwana biyu basuci abinci ba.

Shidai wannan bawan Allah daya debi abincin nan, ya iya tabbatar ma alkali da cewa wallahi kwana biyu ne ba’a aza tukunya a gidansa da sunan dafa abinci ba, saboda tsananin yunwar da ake fama da’ita gashi kuma baida kudin sayen abinci.

Makwancinsa kuma Allah ya hore masa abunda ake dafawa a gidansa watarana harda zubarwa ko a shanya sauran abincin amma bai taba taimakonsa ba, duk da kuwa yasan halin tsananin yunwa da suke fama da’ita, bai taba dibar koda dafaffen abinci ya taimaka masa da sunan ya bama yayansa dake fama da tsananin yunwa ba.

Shine dalilin da yasa ana kare dafuwar abincin gidan makwafcinsa ya lallaba ya debo ya kawoma yayansa dake fama da tsananin yunwa su samu suci.

Shi kuma makwafcin mutum yakaisa kara a kotu akan abimasa hakkinsa na abincin gidansa daya diba ya ciyarda yayansa.

Shine alkali yace ya bada dubu talatin dinda za’a kai wanda yakai kara gidan yari, anan take ya fitarda dubu talatin dinda za’a kai makwancin nasa gidan yari, shi kuma alkalin ya dauki kudin ya bama wanda aka kawo kara ya kara ya sayi abinci.

Views: 73

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *