HOTUNA: “Sabbin hotunan Murja Ibrahim sun tada ƙura a kafafen sada zumunta”

Kamfanin BUA ya rage farashin buhun siminti zuwa ₦3,500 daga gobe Litini.

Kamar yadda Kamfanin yayi alƙawarin rage farashin daga gobe 2 gawatan Oktoba na kayayyakin da kuma bin diddigin ayyukan Lokaci bayan Loakaci don samun inganci tare da tabbatar da ana sayar da kowani buhun siminti na Kamfanin sa akan ₦3,500 a faɗin Nijeriya kamar yadda Jaridar ALFIJIR HAUSA ta bi kanun Lamarin ta kuma tabbatar da sahihancin wannan rahoto.

Bugu da ƙari rukuni na kamfanin BUA ɗin ya ƙara da cewa sun cika alƙawarin da suka ɗauka ne bayan furta hakan ga manema Labarai cikin wasu makonni a baya, “inda kamfanin ya tabbatar cewa tuni ya kammala wannan shiri na tattaunawa kan wannan aniyar ta su dan rage farashin buhun simintin zuwa ₦3,500 na dindin tare da sauran wasu muhimman abubuwa na haɓaka harkan gini har izuwa wannan ƙarshen shekaran.”

Kamfanin ya wallafa hakanne yanzu a babba shafin sa dake dandalin fesbuk mai suna BUA Group domin sanar da abokan hulɗa dasu.

Views: 22

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *