VIDEO: “Labarin yadda wata mata ke sana’ar tura kurar Ruwa a jihar Kano”

WATA UWAR MARAYU SABODA BABU KURAR RUWA TA KE TURAWA😭😭😭

Lokacin da wani ya kirani ya ce mun akwai wata mata a unguwarsu kurar ruwa ta ke turawa ta samowa yaranta abunda za su ci abinci, ban yadda ba don haka na ce idan ya kara ganinta ya mun vedio ya turo mun, ai kuwa washegari ya ganota ya turo mun vedio dinnan.😭😭

Allah ya sani hankalina ya yi matukar tashi, Innalillahi wa’inna ilaihi rajiun, a cikin garin Kano ace mace na garuwa, gidan haya an tasheta a rakabe ra ke a wani guri, ba su da abinci yaranta marayu guda shida babu arabi balle boko, gashi ba ta da halin yin sanaa don babu jari don haka ta nemi kurar ruwa ta ke turawa su samu abunda za su ci abinci da yaranta.

Tabbas wannan tashin hankaline mai sosa zuciya, kuma wai a cikin garin Kano ba kauye ba, al’umma ku taimakawa baiwar Allah nan mu sake mata sanaa, mu kama mata haya mu saka yaranta a makaranta don Allah, babu kadan babu yawa ko dari ce da kai ka taimaka mata, kai koda tayamu yadawa ne har matar nan ta samu taimako shima sadaka ne.
Ga wanda za su taimakawa baiwar Allah nan da yaranta za su iya tura taimakonsu ta account dinmu.

Account no; 0109299375
Account name: Creative Helping Needy Foundation.
Bank name: Access.
Ko
Account name: 6032459122
Account name; Fauziyya Danladi Sulaiman.
Bank name: Keystone.

Ga masu neman Karin bayani za su iya tuntubarmu ta WhatsApp ko message ko kiranmu ta wannan lambar waya. 09128901099
Allah ya baku ikon taimakawa Amin.

Views: 6

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *